Majalisar dattawa ta bayyana dalilan ta na ƙin tantance Abdullahi Ramat

0
15

Majalisar Dattawa ta musanta zargin cewa shugabanninta sun karɓi cin hanci na dala miliyan 10 domin hana tantance Abdullahi Garba Ramat a matsayin shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC).

Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ne ya fitar da sanarwar hakan a Abuja inda ya bayyana zargin da wasu ke yi a matsayin “ɓatanci.”

Ya ce majalisar ta dakatar da tattaunawa kan sunan Ramat ne saboda jerin ƙorafe-ƙorafe da dama na jama’a da na sirri da suka shafi cancantarsa.

> “Majalisa tana da alhakin dakatar da duk wani wanda za’a bawa muƙami da ke fuskantar manyan ƙorafe-ƙorafe har sai an tantance su sosai. Wannan ba sabon abu ba ne,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here