Wata kotun tarayya da ke Abuja ta saka ranar 20 ga Nuwamba domin yanke hukunci a shari’ar da ake yi wa shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, kan zargin ta’addanci.
Alkalin kotun, Justice James Omotosho, ya ayyana ranar ne a yau Juma’a, bayan Kanu ya kasa kare kansa duk da cewa kotu ta ba shi dama sau da yawa ya yi hakan.
An bayyana cewa kotun ta yi wa Kanu dukkan wata damar da doka ta tanada domin ya kare kansa, amma bai yi hakan ba.
Ana sa ran ci gaba da bayani ko ƙarin hukunci daga kotu yayin da ranar yanke hukunci ta kusanto.


