Kamfanin rarraba lantarki na AEDC ya kori ma’aikata 800

0
8

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja (AEDC) ya kori ma’aikatansa 800, a wani mataki na sake fasalin ayyukansa, a daidai lokacin da Najeriya ke fama da karancin wuta da tsadar rayuwa.

Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa kamfanin ya fara da niyyar sallamar ma’aikata 1,800, amma daga baya aka rage adadin zuwa 800 bayan tattaunawa da ƙungiyoyin ma’aikatan lantarki da sauran masu ruwa da tsaki.

Wannan mataki ya zo ne a lokacin da ake fama da tsadar kudin wutar lantarki da matsalar yawan yanke wuta a sassan ƙasar nan, lamarin da ya ƙara jefa jama’a cikin ƙalubale.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here