Za mu yi duk mai yiwuwa wajen daƙile kisan Kiristoci a Najeriya, inji Trump

0
10

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake jaddada ikirarin da ya dade yana yi cewa Kiristoci na fuskantar barazana a Najeriya.

A wani jawabi da ya yi a Fadar White House, Trump ya ce Amurka ba za ta ci gaba da kallon kashe-kashen da ake yi wa Kiristoci a Najeriya da wasu ƙasashe ba tare da ta ɗauki mataki ba.

Ya zargi “masu tsattsauran ra’ayin Musulunci” da ci gaba da kisa da suka yi sanadin dubban rayukan Kiristoci a Najeriya, lamarin da ya sa ya sanya ƙasar cikin jerin waɗanda Amurka ke nuna damuwa a kansu.

Trump ya ce Amurka “a shirye take ta kare Kiristoci a ko’ina cikin duniya,” tare da bayyana cewa ya riga ya umarci Majalisar Wakilan ƙasar da ta gudanar da bincike kan lamarin, sannan ta gabatar masa da rahoto cikin gaggawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here