Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa na ci gaba da tattaunawa da manyan ƙasashen duniya ta hanyar diplomasiyya domin magance ƙalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta.
Tinubu ya bayyana haka ne yayin zaman majalisar ministoci a yau Alhamis, cikin yanayi da ya biyo bayan barazanar tsoma bakin soja da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi, inda ya zargi gwamnati da ƙyale ’yan bindiga suna kashe Kiristoci.
Shugaban ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa gwamnati ba za ta sassauta ba a yaki da ta’addanci.
“Muna tattaunawa da abokan hulɗarmu ta diflomasiyya duk da ƙalubale da fargabar da jama’a ke ciki. Ina tabbatar muku za mu kawo ƙarshen ta’addanci,” in ji Tinubu.
Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da manufofin Sabunta Fata domin gina Najeriya mai kwanciyar hankali da ci gaba.
Wannan shi ne karo na farko da Tinubu ya yi tsokaci kai tsaye kan lamarin tun bayan zargin da Trump ya yi wa Najeriya.


