Hukumar kashe gobara ta Kano ta tabbatar da mutuwar yara biyu da suka faɗa rijiya a ƙananan hukumomin Dawakin Tofa da Dala.
A sanarwar da mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar, ya ce hatsarin farko ya faru ne a safiyar Talata, 4 ga Nuwamba 2025, a kauyen Kashirmo na Dawakin Tofa, inda yarinya ’yar shekara takwas, Zara’u Muhammad, ta faɗa rijiya. Duk kokarin mutanen kauyen kafin isowar ma’aikatan ceto bai yi nasara ba saboda zurfin rijiyar. Daga bisani tawagar ceto ta fitar da gawarta tare da mika ta ga mai unguwa.
Hatsarin na biyu ya faru ne a safiyar Laraba, 5 ga Nuwamba, a Dandishe Tsamiyar Goodluck, Dala LGA, inda yaro ɗan shekara shida, Ahmad Abdurashid, ya faɗa rijiya. An ciro shi rai a hannun ma’aikatan hukumar, amma daga baya aka tabbatar da rasuwarsa.
Daraktan hukumar, Alhaji Sani Anas, ya nuna damuwarsa kan yawan faruwar irin waɗannan lamurra, yana roƙon jama’a su rufe rijiyoyi da kyau kuma kada a bar su a fili ko gefen hanya. Ya kuma shawarci iyaye su kula da motsin ’ya’yansu, musamman ƙanana.


