An rantsar da Paul Biya, mai shekara 93, a matsayin shugaban ƙasar Kamaru karo na takwas, a wani taro da aka gudanar a majalisar dokokin ƙasar da ke Yaoundé.
Biya, wanda ya shafe shekaru 43 yana mulkin ƙasar, zai fara wani sabon wa’adi na shekara bakwai bayan samun kashi 54% na ƙuri’un zaɓe. Abokin takararsa, Issa Tchiroma Bakary, ya samu 35%, a cewar hukumar zaɓe ta ƙasa.
Duk da sakamakon da aka bayyana, Tchiroma Bakary ya yi iƙirarin cewa shi ne ya yi nasara, yana zargin an tafka maguɗi zarge-zargen da hukumomi suka musanta.
Tun bayan bayyana sakamakon zaɓen, rahotanni sun nuna tayar da hankali a wasu yankunan ƙasar, yayin da magoya baya daga bangarori daban-daban ke ci gaba da bayyana martani.


