An kama mutum biyu ’yan jam’iyyar NNPP a Tofa, Jihar Kano, wanda suka haɗar da Murtala Garba Doka da Shamsu Safiyanu Lambu (Shamzeet Lambu), biyo bayan wani rubutu da suka yi a Facebook inda suka soki Shugaban Karamar Hukumar Tofa, Ibrahim Yakubu Addis.
Shamzeet Lambu ya yi zargin cewa shugaban karamar hukumar ya gaza kammala aikin titin Lambu–Banki–Yarimawa–Jakata, wanda ya ce an amince da shi ne kan Naira miliyan 240, tare da jin cewa an tsaya ne kawai a share titi da zuba yashi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban karamar hukumar ne da kansa ya kai korafinsu ga ofishin binciken laifuka (CID). Mutane biyun an fara tsare su a ofishin ’yan sanda na Tofa, daga bisani aka mayar da su hedikwatar ’yan sanda a Bompai domin ci gaba da bincike.
Shugaban matasa na yankin, Nazifi Ado Lambu, ya tabbatar da kamen, wanda ya tayar da hankalin al’ummar yankin, musamman ma wadanda suka daɗe suna neman a kammala aikin titin.
Da aka tuntube shi, Shugaban Karamar Hukumar, Ibrahim Yakubu Addis, ya ce an gayyaci mutanen ne domin su tabbatar da zargin da suka yi, yana mai cewa adadin kudi da suka ambata ba daidai ba ne.
A cewarsa, gwamna ya amince da aikin ne da kudi kasa da Naira miliyan 100, ba miliyan 240 ba.
Lamarin ya janyo muhawara a Tofa, inda jama’a ke kira da a warware matsalar cikin lumana.


