Amurka zata sanya takunkumi ga kungiyoyin fulanin Najeriya

0
25

Majalisar Dokokin Amurka ta fara nazarin wani sabon kudiri da ke neman kakaba takunkumi ga wasu mutane da kungiyoyi da ake zargin suna da hannu a take hakkin ‘yancin addini a Najeriya.

Kudirin, wanda dan majalisar wakilai Smith Christopher ya gabatar, ya ambaci Miyetti Allah da Miyetti Allah Kautal Hore a matsayin kungiyoyin da ake alakanta wa da cin zarafin ‘yancin addini. Kudirin na neman a sanya musu takunkumin shiga Amurka (visa ban) da daskare kadarorinsu.

Christopher ya gode wa Shugaba Donald Trump kan sake sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake kallon suna da matsalar take ‘yancin addini, yana mai zargin gwamnatin Najeriya da gazawa wajen dakile hare-haren tsattsauran ra’ayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here