Najeriya ta yi asarar dala biliyan 300 sakamakon satar ɗanyen man fetur

0
19

Najeriya ta yi asarar dala biliyan 300 sakamakon satar ɗanyen man fetur

Majalisar Dattawa ta gano cewa ƙasar ta yi asara fiye da dala biliyan 300 sakamakon satar man fetur, da rashawa a yankin Neja Delta.

Rahoton wucin gadi na kwamitin bincike ƙarƙashin jagorancin Sanata Ned Nwoko ya bayyana cewa daga 2015 zuwa yanzu, an rasa sama da dala biliyan 200 ba tare da cikakken bayani ba, yayin da aka yi asarar dala biliyan 81 tsakanin 2016 da 2017.

Shugaban Majalisa, Godswill Akpabio, ya yaba da rahoton amma ya ce ikon dawo da kudaden da aka sace ba na majalisa ba ne, sai dai na hukumomin EFCC da ICPC.

Kwamitin ya ba da shawarar amfani da jirage maras matuka don sa ido kan bututun mai, kafa kotunan musamman don hukunta masu satar mai, da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin auna mai na duniya.

Majalisar ta amince da rahoton tare da umartar kwamitin da ya kammala cikakken bincike don dakile satar mai da magance asarar kudaden gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here