Tsohon gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana godiyar sa ga Allah (SWT) yayin da yake bikin cika shekaru 70 a duniya, inda ya bayyana wasu abubuwan da suka faru a lokacin rayuwarsa da kuma darussan da ya gani.
A cikin sakonsa, Shekarau ya nuna matuƙar farin ciki da kuma godiya ga mahaifansa, bisa tarbiyya da ilimin da suka bashi tun yana ƙuruciya, yana mai cewa su ne tushen nasarorinsa a rayuwa.
Ya kuma gode wa ‘yan uwansa, iyalansa, abokan karatunsa, abokan aiki siyasa, masoya da magoya bayansa bisa goyon bayan da suka nuna masa tsawon shekaru. Ya roƙi Allah ya saka musu da alheri.
Shekarau ya ce a tsawon shekarunsa 70 a duniya, yana iya yiwuwa ya taɓa cutar da wasu, ko da da gangan ko ba da gangan ba, don haka ya nemi afuwar duk wanda hakan ta shafa. Haka zalika, ya bayyana cewa shi ma ya yafe wa duk wanda ya taɓa yi masa laifi.
Ya jaddada cewa tun daga farko rayuwarsa ta kasance bisa ka’idar gaskiya da ladabi, bisa koyarwar addinin Musulunci, musamman a lokacin da yake gudanar da harkokin gwamnati da na jama’a.
Shekarau ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rayu cikin bin koyarwar addini, yana mai cewa “kyawon rayuwa ba a cikin yawan farin ciki da mutum ke ciki yake ba, sai dai yadda mutane suke farin ciki da gudunmawar da ka bayar a rayuwarsu.”
Yayin da yake tuna matashinsa, tsohon gwamnan ya bayyana yadda yake cikin ƙungiyoyin Musulmai a lokacin makaranta da kuma yadda aikin NYSC ɗinsa a Jihar Imo ya zame masa babbar hanya ta kwarewa da fahimtar rayuwa.
A ƙarshe, Shekarau ya shawarci matasa da su kasance masu ƙwazo, gaskiya, da jajircewa a duk abin da suka sa gaba.


