Majalisar dattawan Najeriya ta amince da karatu na biyu kan kudirin neman kafa doka da manufofi don sauya tsarin sufuri daga amfani da motoci masu amfani da man fetur zuwa na lantarki.
Sanata Orji Uzor Kalu, wanda ya dauki nauyin kudirin, ya bayyana cewa manufar dokar ita ce rage hayakin da ke gurbata muhalli, karfafa masana’antar kera motoci a cikin gida, tare da bai wa Najeriya damar shiga cikin kasuwar duniya da ke komawa kan fasahar sufuri mai tsafta.
Kalu ya ce sashin sufuri yana da alhakin kusan kashi 20 zuwa 30 cikin 100 na hayakin da ke haifar da dumamar yanayi a Najeriya, yana mai gargadin cewa kasar na iya barin sauran kasashen Afrika su gabace ta idan ba a dauki mataki ba.
“Wannan kudiri zai samar da cikakken tsarin doka da cibiyoyi da za su jagoranci canjin Najeriya daga dogaro da motoci masu amfani da man fetur zuwa na zamani da ke amfani da makamashin lantarki mai tsafta da kare muhalli,” in ji shi.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana kudirin a matsayin “abu mai kyau” tare da fatan ganin yadda za a aiwatar da shi nan gaba.
An mika kudirin ga Kwamitin Majalisar kan Masana’antu, wanda ake sa ran zai gabatar da rahotonsa cikin makonni hudu.


