Jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a Jos, ya hallaka mutane biyu

0
7

Wani mummunan hatsarin jirgin ƙasa ya afku a yankin Phototake da ke cikin birnin Jos, jihar Filato, inda jirgin ya murƙushe wani babur mai ƙafa uku, kuma hakan ya yi sanadin mutuwar mutum biyu, tare da jikkata wasu mata biyu.

Rahoton jaridar Daily Trust ya bayyana cewa, jirgin ƙasan ya taso ne daga Bukuru zuwa Jos babban birnin jihar a safiyar yau Laraba, lokacin da ya gamu da babur ɗin a hanya.

Wani ganau da ya shaida lamarin ya ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na safe, inda direban babur ɗin da wani fasinja suka rasa rayukansu nan take, yayin da wasu mata biyu suka samu raunuka masu tsanani.

A cewar wani mazaunin yankin, rashin kula daga wanda ke da alhakin rufe shingen tsallaka titin jirgin a kusa da shataletalen Phototake Abattoir shi ne ya haddasa wannan mummunan lamari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here