Shugaban ƙasa Tinubu zai ciyo sabon bashi

0
18

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi majalisar dokokin ƙasa ta amince masa ya ciyo sabon bashin Naira tiriliyan 1.15, domin cike gibin da ke cikin kasafin kuɗin shekarar 2025.

Bisa wata wasiƙa da aka karanta a gaban majalisar dattawa yayin zaman ranar Talata, shugaban ƙasar ya bayyana cewa wannan lamuni zai taimaka wajen aiwatar da shirye-shiryen gwamnati da ayyukan ci gaba da aka tsara a kasafin kuɗin bana.

Shugaban majalisar dattawa ya tura buƙatar zuwa kwamitin lamunin cikin gida da na waje na majalisar domin nazari, tare da umartar su dawo da rahoton su cikin mako guda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here