Mai laifi ya gudu daga gidan gyaran hali, bayan ya ɗaure masu gadin sa a Kano

0
17

Babbar Kotun Jihar mai lamba biyu da ke Sakatariyar Audu Bako a Kano, karkashin jagorancin Mai Shari’a Yusuf Ubale Muhammad, ta yanke wa wani matashi mai suna Jamilu Tukur hukuncin daurin shekaru 20 a gidan gyaran hali, bayan an same shi da laifin fashi da makami da hada kai wajen aikata laifi.

Rahotonni sun ce lamarin ya faru ne tun a shekarar 2021, lokacin da Jamilu tare da abokinsa suka kwace wa wata mata mai suna Bilkisu Haruna waya a kan hanyar zuwa gidan Zoo, bayan sun zare mata huka.

Lauyar gwamnati, Barista Hafsat Kabir Sunusi, ta gabatar da shaida biyar a gaban kotu, yayin da wanda ake tuhuma ya kare kansa ta hannun lauyansa, Barista Nasir Ibrahim.

Bayan sauraron hujjojin bangarorin biyu, kotu ta gamsu da shaidun masu gabatar da kara, inda ta same shi da laifi, ta kuma yanke masa hukuncin daurin shekaru 20 tare da biyan tarar Naira 50,000. Haka kuma, an ƙara masa hukuncin daurin wata shida ko kuma biyan tara Naira 10,000.

A yayin da ake ci gaba da shari’ar, jami’an gidan gyaran hali sun shaida wa kotu cewa wani abokin laifinsa, Usman Aliyu, ya gudu daga gidan yarin yara na Goron Dutse bayan ya daure masu gadin gidan tare da jikkata su.

Kotun ta umarci Darakta na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da kuma Kwamishinan ‘Yan Sanda na Kano da su kamo Usman Aliyu domin a dawo da shi gidan gyaran hali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here