Kotu ta umarci Damagum ya Jagoranci babban taron PDP

0
10

Wata babbar kotu a jihar Oyo ta bayar da umarni ga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da shugaban ta na rikon kwarya Umar Damagum, da su ci gaba da shirye-shiryen gudanar da taron gangamin jam’iyyar wanda za’a yi a ranar 15 ga Nuwamba a birnin Ibadan.

Mai shari’a A.L. Akintola ne ya bayar da wannan umarni bayan ya saurari bukatar wucin gadi da wani dan jam’iyyar, Folahan Malomo Adelabi, ya gabatar a kotu.

Adelabi ya roki kotu da ta hana wadanda ake tuhuma ciki har da PDP, Damagum, gwamnan wani jiha Umar Fintiri, da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) daga yin wani abu da zai hana gudanar da taron.

A cewar karar, ana son kotu ta tabbatar da cewa shugabannin jam’iyyar za su bi jadawalin da aka tsara don gudanar da taron, wanda za’a zabi sababbin shugabannin jam’iyyar a matakin kasa.

Kotun ta amince da bukatar, inda ta umurci jam’iyyar PDP da ta ci gaba da bin dokokin jagoranci da jadawalin da ta tsara domin taron gangamin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here