Kiristoci ne ke kashe mutane a kudu–Gwamnan Anambra

0
10

Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, ya karyata ikirarin shugaban Amurka, Donald Trump, cewa ana kashe Kiristoci a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

A wata hira da aka yi da shi a tashar Channels TV, Soludo ya bayyana cewa rikice-rikicen da ke faruwa a yankin kudu ba na addini ba ne, domin duka masu kai hare-hare da wadanda abin ya shafa Kiristoci ne.

> “Mutane ne ke kashe junansu. Kiristoci suna kashe Kiristoci,” in ji Soludo, yana mai cewa sama da kashi 95 cikin ɗari na mutanen yankin Kiristoci ne.

Ya ce matsalolin siyasa, zamantakewa da tattalin arziƙi ne ke haddasa tashin hankali a yankin, ba bambancin addini ba.

Gwamnan ya kuma yi kira ga gwamnatin Amurka da ta binciki gaskiyar zargin kafin yin wasu kalamai game da Najeriya, yana mai gargadi cewa irin wadannan maganganu na iya haddasa karin rikici.

Soludo ya jaddada cewa hanyoyin da za su kawo zaman lafiya sun haɗa da tattaunawa, adalci da shugabanci nagari. Ya roki shugabannin siyasa da al’umma a Kudu maso Gabas da su haɗa kai don warware matsalolin yankin cikin lumana.

> “Abin da muke bukata shi ne fahimta da haɗin kai, ba kalamai masu tayar da hankali ba,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here