Hukumar Tsaron Farin kaya ta ƙasa (DSS) ta sanar da korar jami’ai 115 daga cikin ma’aikatanta, a wani yunkuri na ci gaba da gyara da tsaftace hukumar.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Talata, DSS ta gargadi jama’a da su guji yin mu’amala da waɗannan jami’an da aka kora bisa sunan hukumar, domin ba su da wani hurumi ko alaka da ita daga yanzu.


