China ta ja kunnen Amurka a kan shiga harkokin Najeriya

0
13

Gwamnatin kasar China ta bayyana cikakken goyon bayan ta ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tana mai cewa tana tallafawa Najeriya yayin da take jagorantar al’umarta kan tafarkin cigaba da ya dace da yanayin ta na cikin gida.

Da take magana a taron manema labarai a yau Talata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar, Mao Ning, ta ce: “A matsayinta na abokiyar hulɗa ta dabaru da tattalin arziki da Najeriya, China tana adawa da kowace ƙasa da ke amfani da addini ko kare haƙƙin ɗan adam a matsayin hujja don tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wasu, ko kuma yin barazanar kakabawa wasu ƙasashe takunkumi ko amfani da ƙarfi.”

Mao Ning ta yi wannan jawabi ne a lokacin da take mayar da martani kan barazanar Shugaban Amurka Donald Trump na kai farmaki a Najeriya bisa zargin cin zarafin Kiristoci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here