Sojojin haɗin gwiwa na Operation MESA sun dakile harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Shanono, Jihar Kano.
Bisa bayanan sirri da aka samu kan motsin ‘yan bindiga a unguwannin Ungwan Tudu, Ungwan Tsamiya da Goron Dutse a ranar 1 ga Nuwamba 2025 da misalin ƙarfe 5 na yamma, dakarun sojin tare da sauran jami’an tsaro suka kai samame, inda suka fatattaki ‘yan bindigar bayan musayar wuta mai zafi, kamar yadda Kyaftin Babatunde Zubairu, Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a, Rundunar Soji ta 3 Brigade, ya sanar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun iso yankin ne a kan babura, inda sojojin suka kashe mutum 19 daga cikinsu. Haka kuma, an kwato babura da dama da wayoyin salula guda biyu. Sai dai rundunar ta tabbatar da cewa sojoji biyu da ɗan sa-kai ɗaya sun rasa rayukansu a yayin artabu da ‘yan ta’addan.
Sanarwar tace rundunar ta ci gaba da gudanar da bincike da aikin tsaro a yankin domin kare al’umma daga hare-haren ‘yan fashi da satar shanu. Sojin Najeriya sun bukaci jama’a da su ci gaba da kasancewa cikin shiri da kuma sanar da hukumomi duk wani motsin da suka yi zargin zai cutar.
Kwamandan 3 Brigade, Birgediya Janar Ahmed Tukur, ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar sojin Najeriya za ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kano da ma ƙasar baki ɗaya.


