Matar aure ta yi amfani da wuƙa wajen yanka wuyan mijin ta a Neja 

0
11

An kama wata matar aure mai suna Halima Salisu a garin Kuta, cikin Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja, bisa zargin yanka wuyan mijinta, Salisu Suleiman, da wuƙa yayin da yake barci.

Majiyoyi sun bayyana cewa bayan ta yankar masa wuya, ta kuma soka masa wuƙa a idonsa na hagu wanda ya lalata idon gaba ɗaya. Rahotanni sun ce saɓani tsakanin ma’auratan ne ya haifar da wannan mummunan lamari.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin da safiyar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025. Ya ce an kai wanda abin ya faru da shi Asibitin Gabaɗaya na Kuta, daga bisani aka tura shi Asibitin Ƙwararru na IBB da ke Minna domin kulawar likitoci.

An kama Halima Salisu, kuma tana tsare a hannun ‘yan sanda domin gudanar da bincike kafin a gurfanar da ita a kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here