Jami’an tsaro sun mamaye sakatariyar jam’iyar PDP

0
9

An samu tsauraran matakan tsaro a sakatariyar jam’iyyar PDP da ke Abuja, bayan da aka naɗa mataimakin shugaban jam’iyyar na Arewa ta Tsakiya, Abdulrahman Mohammed, a matsayin shugaban rikon kwarya na jam’iyyar.

Kwamitin gudanarwa ƙarƙashin jagorancin Samuel Anyanwu ne ya sanar da wannan naɗi, bayan dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Umar Damagum.

Rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP ya ƙara tsananta ne tun bayan da Damagum tare da wasu mambobin kwamitin gudanarwa suka dakatar da babban sakataren jam’iyyar na ƙasa, Samuel Anyanwu da wasu mambobi.

Sai dai ɓangaren Anyanwu ya maida martani, inda shi ma ya dakatar da Damagum, sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, da wasu mutane huɗu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here