JAMB ta ƙara wa’adin bayar da gurbin karatu a jami’o’in gwamnati

0
12

Hukumar Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandare (JAMB) ta sanar da ƙarin wa’adin kammala karɓar ɗaliban shiga jami’o’in gwamnati daga ranar 31 ga Oktoba zuwa 17 ga Nuwamba, 2025.

A sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin bai wa jami’o’i ƙarin lokaci su kammala tsarin karɓar ɗalibai, sakamakon wasu dalilai da suka taso.

Hukumar ta tunatar da cewa a taron da aka gudanar ranar 18 ga Yuli, ƙarƙashin jagorancin Ministan Ilimi, Dr. Maruf Alausa, an amince da ranar 31 ga Oktoba a matsayin wa’adin ƙarshe na karɓar ɗalibai.

Sai dai JAMB ta ce ƙungiyar shugabannin jami’o’i (AVCNU) ta nemi a ƙara wa’adin saboda wasu matsaloli da suka haɗa da umarnin kotu da ya dakatar da ci gaba da aikin tantancewa, wanda aka ɗaga ranar 28 ga Oktoba, 2025.

Haka kuma, Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta amince da sabbin shirye-shirye 229 a jami’o’i 37, wanda hakan ya ƙara buƙatar lokaci wajen shiryawa da karɓar ɗalibai.

JAMB ta yaba wa jami’o’in gwamnati bisa haɗin kai da jajircewarsu, tana mai cewa ƙarin wa’adin zai tabbatar da adalci da daidaito a tsarin karɓar ɗalibai.

Hukumar ta jaddada cewa sabon wa’adin na Nuwamba 17, 2025, shi ne na ƙarshe, kuma jami’o’i su bi shi a tsanaki domin tabbatar da tsarin karɓar ɗalibai mai gaskiya da sahihanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here