Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC) ta sanar da shirinta na gudanar da zaɓen cike gurbi domin maye gurbin kujerun kansiloli biyu da suka rasu a jihar.
Shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawal Malumfashi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin. Ya ce Kansiloli da abin ya shafa su ne na unguwar Kofar Mazugal a ƙaramar hukumar Dala da kuma Matan Fada a ƙaramar hukumar Ghari.
Farfesa Malumfashi ya bayyana rasuwar kansilolin a matsayin babban rashi ga al’umma, inda ya mika ta’aziyya ga Gwamnatin Jihar Kano da iyalan mamatan.
Ya ce bisa ga tanadin dokar zaɓe ta 2022 da kundin tsarin mulki na 1999, hukumar tana da hurumin gudanar da zaɓen cike gurbi don tabbatar da cewa wakilci ya ci gaba da gudana.
KANSIEC ta bayyana cewa an tsara gudanar da zaɓen a ranar 13 ga Disamba, 2025, kuma shirye-shirye suna tafiya domin tabbatar da sahihancin zaɓen.
Hukumar ta roƙi jam’iyyun siyasa da shugabannin al’umma su bayar da hadin kai wajen gudanar da zaɓe cikin zaman lafiya da gaskiya.
Farfesa Malumfashi ya jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da bin ƙa’idar dimokuraɗiyya, domin tabbatar da cewa muradun al’umma a mazabu biyu sun sami wakilci na gaskiya.


