Gwamnatin Jihar Kano ta amince da shirin mallakar mafi yawan hannayen jarin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO), domin inganta samar da wuta, ƙarfafa masana’antu, da faɗaɗa damar samun ingantacciyar wutar lantarki a fadin jihar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa wannan mataki zai bai wa jihar damar taka muhimmiyar rawa a harkokin samarwa, jigila da rarraba wutar lantarki, domin inganta aiki yadda ya kamata, samar da gaskiya da kuma ingantacciyar hidima ga al’umma.
Haka kuma, shirin na da nufin ƙarfafa tattalin arzikin jihar, samar da ayyukan yi, da jawo hankalin ‘yan kasuwa na cikin gida da na ƙasashen waje.
Bugu da ƙari, Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta amince da gabatar da kuma karɓar Manufar Wutar Lantarki ta Jihar Kano, ƙarƙashin Ma’aikatar Wuta da Sabbin Hanyoyin Samar da Makamashi.


