Mai taimakawa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan harkokin labarai, Temitope Ajayi, ya karyata rahoton da ke cewa Tinubu zai tafi Amurka don ganawa da Mataimakin Shugaban Ƙasar J.D. Vance.
Ajayi ya bayyana a shafinsa na X cewa labarin karya ne, yana mai cewa idan Tinubu zai je White House, zai gana ne da Shugaba Donald Trump, ba da mataimakinsa ba.
Rahoton ya fito ne bayan barazanar Trump cewa Amurka na iya kai hari a Najeriya saboda zargin kisan Kiristoci.
A martani, Tinubu ya musanta zargin, yana cewa Najeriya ƙasa ce ta dimokuraɗiyya da ke mutunta ‘yancin addini da zaman lafiya tsakanin Musulmai da Kiristoci.
Ya jaddada cewa gwamnatin sa na ci gaba da tattaunawa da shugabannin addinai domin tabbatar da jituwa da tsaro a ƙasar.


