Shugaban Amurka, Donald Trump, ya jaddada yiwuwar Amurka ta tura dakarunta Najeriya ko ta kai hare-hare domin dakile abin da ya kira kisan Kiristoci a ƙasar.
Yayin da yake magana da manema labarai, Trump ya ce ba zai bari a ci gaba da kashe Kiristoci a Najeriya ba, yana mai cewa “Ana kashe Kiristoci da yawa a Najeriya, kuma ba zan lamunta da hakan ba.”
Sai dai gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tana maraba da haɗin kan Amurka wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi, amma ta musanta cewa Kiristoci ne kaɗai ake kashewa a hare-haren da ƙasar ke fuskanta daga ƴan ta’adda.
A watan da ya gabata, Amurka ta saka Najeriya cikin jerin ƙasashen da take nuna damuwa da su kan take hakkin yin addini.
A wani saƙo da Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ranar Asabar, ya ce Washington na iya amfani da ƙarfin soja domin murƙushe “ƴan ta’adda masu kishin Islama” da ke aikata ta’asa a Najeriya.


