Ya kamata gwamnatin Kano ta mutunta ƴancin ƴan jarida–Muhammad Garba

0
14

Tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano, Malam Muhammad Garba, ya shawarci Gwamnatin Jihar Kano da ta girmama ‘yancin kafafen yaɗa labarai maimakon tsoratar da ‘yan jarida.

A wata sanarwa da ya fitar a Abuja, Garba ya ce dimokuraɗiyya na bunƙasa ne idan gwamnati ta rungumi gaskiya, haƙuri da tattaunawa da kafafen labarai. Ya bayyana cewa “’Yancin jarida ana auna shi ne da ikon su ruwaito ba tare da tsoro ko ramuwar gayya ba, ba da kyaututtuka ko jawabai ba.”

Garba ya mayar da martani ne kan rahoton cibiyar binciken ayyukan jarida ta Wole Soyinka (WSCIJ) wadda ta sanya Kano cikin jihohin da suka fi karya ‘yancin jarida a Najeriya.

Ya nuna damuwa kan kama wa da tsare ‘yan jarida da dama a Kano, ciki har da Jafar Jaafar na Daily Nigerian, Ibrahim Ishaq Dan’uwa Rano, Buhari Rano, Ismail Auwal da Abdulaziz Aliyu, tare da harin da aka kai wa ma’aikatan Channels TV a watan Agusta 2024.

Garba ya soki dokokin gwamnati da ke takaita shirye-shiryen siyasa kai tsaye da hana tambayoyi masu muhimmanci, yana cewa hakan na nuna danniya da rashin amincewa da ra’ayoyi daban-daban.

Ya bukaci gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta rungumi kafafen labarai a matsayin abokan haɗin kai wajen gina demokuraɗiyya, ba abokan gaba ba.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here