Sanatan Kaduna ta kudu ya bayyana dalilin sa na komawa jam’iyyar APC 

0
9

Sanata mai wakiltar Kaduna ta Kudu, Barista Sunday Marshall Katung, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Wannan mataki nasa ya zo ne sama da awa 24 bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da PDP daga gudanar da babban taronta na kasa na 2025.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Sanata Katung ya bayyana cewa matakin nasa ya samo asali ne daga “burinsa na yi wa mazabarsa aiki cikin inganci” tare da “haɗa kai da shugabannin gwamnati don samun ci gaba mai ɗorewa.”

Ya ce ya yi dogon tunani da shawara da magoya baya, iyalai, da abokai kafin yanke wannan hukunci, yana mai cewa:

“Wannan sauyin siyasa ba don son zuciya ba ne, amma saboda muradin ganin muryar mutanenmu ta ƙara ƙarfi a matakin yanke shawara.”

Katung ya yaba da irin goyon bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani ke bayarwa wajen samar da ci gaba a yankin Kaduna ta Kudu.

Sanatan ya roƙi magoya bayansa da sauran abokansa da su fahimci matakin nasa, yana mai cewa bambancin ra’ayi bai kamata ya raba abokai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here