Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta ƙasa (NARD) ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani, sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen aiwatar da alkawuran da ta dauka.
Shugaban kungiyar, Muhammad Suleiman, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar, bayan taron majalisar koli ta kungiyar (NEC) da aka gudanar makon da ya gabata.
A cewar Suleiman, an dauki wannan mataki ne saboda rashin cika alkawurra da gwamnati ta yi bayan dogon tattaunawa da gargadi da dama.
Likitocin suna neman karin albashi mai kyau, biyan bashin albashi, inganta yanayin aiki, daukar karin ma’aikata, da samar da kayan aikin lafiya da suka dace.
Sun kuma bukaci karin kashi 200 cikin 100 a tsarin albashin likitoci (CONMESS), aiwatar da sabbin alawus-alawus da aka tsara tun watan Yuli 2022, da cire matsalolin takardu da ke hana maye gurbin likitocin da suka bar aiki.
Kungiyar ta bayyana cewa bukatunsu ba na son kai ba ne, sai dai don tabbatar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya a Najeriya.


