Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan jawabin shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya zargi cewa ana kashe Kiristoci a ƙasar.
Trump ya bayyana Najeriya a matsayin “ƙasar da ake da damuwa a kanta,” inda ya ce Kiristanci na fuskantar barazana saboda, a cewarsa, “dubban Kiristoci ana kashe su ta hannun masu tsattsauran ra’ayin Islama.” Ya ƙara da cewa ya umarci wasu ‘yan majalisar wakilan Amurka, Riley Moore da Tom Cole, su gudanar da bincike kan lamarin.
Sai dai a martanin da ta fitar, ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta musanta zargin, tana mai cewa ba gaskiya ba ne.
A cewar kakakin ma’aikatar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, “Najeriya na gode wa ƙasashen duniya bisa kulawarsu, amma batun cewa ana kashe Kiristoci a ƙasar ba gaskiya bane. Duk ‘yan Najeriya na da ‘yancin yin ibada yadda suka ga dama, ba tare da wani wariya ko tsangwama ba.”
Gwamnatin ta ƙara da cewa ƙarƙashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu, ana ƙoƙarin tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma ba tare da nuna bambanci ba.
Ta kuma jaddada cewa Najeriya za ta ci gaba da hulɗa da Amurka da sauran ƙasashen duniya wajen neman zaman lafiya da haɗin kai mai ɗorewa.


