Rundunar sojin ƙasa ta yiwa manyan sojoji 67 sauyin wajen aiki

0
4

Rundunar sojin Najeriya ta yi sabbin sauye sauye inda ta tura manyan hafsoshi 67 zuwa sabbin wuraren aiki a fannonin daban-daban na rundunar.

Wannan sauyin ya shafi manyan hafsoshi 56 masu mukamin Manjo janar da kuma 11 masu mukamin Brigadier-General.

Wata takarda da rundunar ta fitar ranar 30 ga Oktoba, wacce Babban Sakatare na sojoji, EL Okoro ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa sabbin wuraren aiki za su fara aiki daga ranar 3 ga Nuwamba, 2025.

A cewar takardar, dukkan kwamandoji da wannan sauyin ya shafa an umurce su da su karɓi sabbin mukamansu a kan lokaci, kuma a sanar da sashen ma’aikata na rundunar bayan karɓar aiki.

Haka kuma, an gargadi kwamandoji da za su ki sakin jami’an da aka tura, ko wadanda ba za su je sabbin wuraren aikinsu akan lokaci ba, cewa za a ɗauki mataki a kansu.

Daga cikin manyan hafsoshin da aka bar su a wurin aikinsu amma aka ba su sabbin mukamai akwai Major-General P.A.O Okoye, Y. Yahaya, I. Otu, da S. Nuhu.

Wannan sauyin ya zo ne kwanaki bayan Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da sauye-sauye a manyan mukaman tsaron ƙasar, inda ya naɗa Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon Babban Hafsan Tsaro, yayin da Waidi Shaibu, Sunday Aneke, da Idi Abbas suka zama shugabannin rundunar ƙasa, sama, da ruwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here