Babbar kotun jiha dake Miller Road a Kano, karkashin jagorancin Mai Shari’a Musa Dahiru, ta tura wani magidanci mai suna Idris Kurma gidan gyaran hali, bisa zargin kashe matarsa saboda taki daka masa kuli-kuli kamar yadda ya bukata.
An gurfanar da Kurma a gaban kotu bisa zargin aikata laifin kisan kai, wanda ya saba da sashi na 221 na kundin hukunta laifuka. Lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba Soron Dinki, ne ya gabatar da karar, inda wanda ake tuhuma ya musanta aikata laifin da ake zarginsa da shi.
Lauyan gwamnati ya roki kotu ta ba su lokaci domin gabatar da shaidu, yayin da lauya mai kare kurma, Barista Ibrahim Adakawa, ya bukaci kotu ta ba su cikakken bayani kan shari’ar.
Kotun ta amince da rokon bangarorin biyu, tare da sanya ranar 12 ga watan Disamba, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar.
Rahotanni sun nuna cewa, ana zargin Idris Kurma da kashe matarsa, Aisha Idris, a garin Goda dake karamar hukumar Shanono, bayan ta ki daka masa kuli-kuli, inda ake zargin ya shake ta har ta mutu.


