Kotu ta dakatar da babban taron PDP na kasa

0
6

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin dakatar da jam’iyyar PDP daga gudanar da babban taronta na kasa da aka shirya a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba a Ibadan, jihar Oyo.

Mai shari’a James Omotosho ne ya yanke wannan hukunci a ranar Juma’a, inda ya bayyana cewa jam’iyyar ta karya kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, da na hukumar INEC, da kuma nata tsarin mulkin, saboda gazawar gudanar da sahihin zaɓe a jihohi kafin shirya taron kasa.

A cewar alkalin, ci gaba da shirya taron ba tare da gyara wadannan kura-kurai ba zai zama take doka da kuma saba wa tsarin dimokuradiyya a cikin jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here