Dole ce ta sanya na gayyaci Akpabio zuwa wajen ƙaddamar da aiki–Natasha
Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bayyana cewa gayyatar da ta aikewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da sauran ‘yan majalisa domin halartar bude ayyuka a jiharta, ta biyo hanyar doka da tsarin majalisa, ba don wata manufa ta kashin kai ba.
Akpoti-Uduaghan ta yi wannan bayani ne a ranar Alhamis, bayan ta gayyaci shugaban majalisar da wasu sanatoci zuwa bikin kaddamar da wasu ayyuka da ta gudanar a Kogi, watanni biyu bayan dawowarta daga dakatarwa.
Ta ce ta rubuta wasikar gayyatar ne ta hannun shugaban zaman majalisar, domin a karanta a zauren majalisar kamar yadda tsarin majalisa ya tanada.
Sanatar ta kara da cewa wannan mataki nata yana nuna bin doka da girmama cibiyoyin gwamnati, tare da bayyana cewa kaddamar da ayyukan ba don nuna kai ba ne, illa hidima ga jama’ar da take wakilta.


