An saka lokacin fara karɓar sabon harajin kaso 5 na man fetur

0
18
man fetur
man fetur

Shugaban kwamitin sake fasalin haraji na shugaban ƙasa, Taiwo Oyedele, ya ce ba za a fara aiwatar da harajin mai na kashi 5% ba sai naira ta ƙarfafa ko farashin danyen mai ya faɗi.

Ya bayyana cewa manufar harajin ita ce a tara kuɗaɗen gyaran hanyoyi, amma aiwatar da shi yanzu zai ƙara wa ‘yan ƙasa wahala.

Oyedele ya ce tsarin harajin ya samo asali tun lokacin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, kuma ƙasashe sama da 150 suna yin irinsa.

Ya ƙara da cewa kwamitinsu ya ƙi amincewa da buƙatar hukumar FERMA ta fara karɓar kuɗin, saboda yin hakan yanzu “ba zai dace da halin tattalin arzikin ƙasa ba.”

A cewarsa, gwamnati za ta fara ne kawai idan al’amuran tattalin arziki suka daidaita, tare da tabbatar da cewa gyaran haraji zai rage haraji masu yawa da ke damun ‘yan kasuwa da masu sufuri.

A kwanan nan ne aka samu labarin cewa za’a fara karɓar harajin kaso 15 akan man fetur da aka shigo da shi daga ketare

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here