Rikicin Limancin Masallacin Juma’a Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 2 a Taraba
Akalla mutane biyu sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata a rikicin da ya barke kan shugabancin babban masallacin Juma’a na Donga, a jihar Taraba.
Rahotanni sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne a ranar Talata bayan sabani ya taso tsakanin mambobin al’umma musulmi kan wanda ya dace ya jagoranci masallacin.
An ce rikicin ya rikide zuwa tashin hankali tsakanin bangarori biyu, inda aka lalata kadarori da dama kafin jami’an tsaro su shiga tsakani.
Wani mazaunin garin ya shaida cewa dakarun tsaro, ciki har da sojoji, sun isa yankin domin dawo da doka da oda.
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Taraba, ASP Leshen James, bai amsa kiran waya ko sakon da aka aike masa domin jin karin bayani ba.


