Hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta ƙasa (JAMB) ta bayyana cewa ma’aikatanta fiye da goma suna fuskantar shari’a bisa zargin cin hanci da rashawa.
Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana hakan a taron ƙungiyar ma’aikatan jami’o’i ta ƙasa NASU da aka gudanar a Abuja, inda ya ce JAMB tana ɗaukar nauyin walwalar ma’aikata da ladabi a matsayin ginshiƙan aiki.
Ya ce, duk da ƙoƙarin inganta rayuwar ma’aikata, hukumar ba ta sassauta hukunci ga masu laifi ba.
Oloyede ya kuma soki iyaye da ke amfani da kuɗi ko matsayin su wajen samun guraben karatu ga yaransu, yana mai cewa hakan na lalata tsarin ilimi, musamman yadda ake gaggawar tura yara ƙanana makarantu.
Ya ƙara da cewa JAMB ta kafa ƙa’idar shekarun shiga jami’a a kalla 16 domin kare yara.


