Wasu ’yan bindiga sun kai hari a garin Kurawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto, inda suka kashe mutane uku, ciki har da mukaddashin hakimin garin.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shiga garin ne da misalin ƙarfe 12 na daren Alhamis, inda suka fara harbe-harbe bayan sun karya katangar da mazauna yankin suka gina domin tsaro.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Mun samu kiran waya daga wani kauye da ke makwabtaka da mu cewa ’yan bindiga na tahowa. Nan da nan muka sanar da hukumomin tsaro. Amma kafin su iso, maharan sun shiga ta bangaren da suka karya katanga suka fara harbi.”
Tuni an binne waɗanda suka mutu da safiyar Alhamis.
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa wannan ne karo na 20 da ’yan bindiga ke kai hari a Kurawa cikin ’yan shekarun nan.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmed Rufa’i, bai amsa kiran waya ko sakonnin da aka turo masa ba har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto.


