Gwamnatin Bauchi ta ƙirƙiro sabbin ƙananun hukumomi 29

0
23

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya rattaba hannu kan dokar ƙirƙirar ƙarin ƙananan hukumomi 29 a cikin jihar.

Wani takarda da Daily Trust ta samu ta nuna cewa Mukaddashin Magatakardan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Musa Yerima, ya aika da bukatar majalisar ga Kwamitin Sauya Kundin Tsarin Mulki na Majalisar Dattawa, domin neman amincewar Majalisar Tarayya a cikin gyaran kundin tsarin mulki da ake gudanarwa yanzu.

A halin yanzu, Bauchi na da ƙananan hukumomi 20 da kundin tsarin mulki na 1999 ya amince da su. Da ƙarin da aka tsara, yawan ƙananan hukumomin zai kai 49, a cikin jihar da ake hasashen tana da yawan jama’a kimanin miliyan 10.

A wasikar da Yerima ya aika wa Sanata Barau Jibrin, wanda ke jagorantar kwamitin sauya kundin tsarin mulki, ya ce:

> “Ina farin cikin sanar da kai cewa Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta amince da dokar ƙirƙirar ƙarin ƙananan hukumomi 29 a jihar. Dokar za ta fara aiki ne bayan Majalisar Tarayya ta amince da ita, kamar yadda sashe na 8(5) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (da aka yi wa gyara) ya tanada.”

Ya ƙara da cewa:

> “Wannan dokar ta samu amincewa bisa tanadin sashe na 100(3) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999.

Idan Majalisar Tarayya ta amince, Bauchi za ta zama ɗaya daga cikin jihohi mafi yawan ƙananan hukumomi a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here