An Gudanar da Jana’izar Kwamandan Yaki da Ƙwacen Waya na Kano

0
7

An gudanar da jana’izar marigayi Inuwa Salisu, kwamandan kwamitin yaƙi da masu ƙwacen waya na jihar Kano, a unguwar Sharada.

Taron jana’izar ya samu halartar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da wasu jami’an gwamnati, ƴan uwa da abokan marigayin, wadanda suka bayyana jimaminsu kan rasuwar tasa.

Rahotanni sun ce wasu ɓatagari ne suka kai masa hari a gidansa da ke Sharada a daren ranar Talata, inda suka kashe shi.

Hukumomi sun ce ana ci gaba da bincike domin gano wadanda suka aikata wannan aika-aika.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here