Wasu Gwamnonin PDP na shirin komawa jam’iyyar APC

0
5

Ana ƙara nuna damuwa a kan cewa Najeriya na iya komawa tsarin jam’iyya ɗaya, bayan da jam’iyyar PDP wacce ta daɗe tana da rinjaye a siyasar ƙasar ke ci gaba da rasa manyan ‘ya’yanta ga jam’iyyar APC mai mulki.

Rahotanni daga jaridar The Punch sun nuna cewa gwamnonin PDP huɗu daga Arewa na tunanin sauya sheƙa zuwa APC kafin zaɓen 2027. 

Tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999, PDP ce ke da rinjaye har tsawon shekaru 16 tana mulkin ƙasa, amma yanzu tana da gwamnonin jihohi takwas kacal, da suka hadar da Bauchi, Oyo, Adamawa, Osun, Plateau, Taraba, Zamfara da Rivers.

Jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana yiwuwar sauyin sheka daga wasu manyan jami’an jam’iyyun adawa na PDP da Labour Party, inda ake rade-radin cewa akalla gwamnoni huɗu na tattaunawa da ita domin komawa cikinta.

Mataimakin Shugaban APC na ƙasa mai kula da yankin Kudu maso Gabas, Dakta Ijeoma Arodiogbu, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da jaridar The PUNCH.

Punch, tace gwamnonin Taraba, Adamawa da Zamfara na cikin waɗanda ake zargin zasu sauya shekar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here