Wasu ƴan ƙasashen waje sun nemi damar zama ƴan Najeriya—Gwamnatin tarayya

0
21
Bola Tinubu
Bola Tinubu

Ministan Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa fiye da mutane 170 daga kasashen waje ne suka nemi samun damar zama ’yan kasa na Nijeriya.

Tunji-Ojo ya bayyana hakan ne a shafinsa na X bayan ya jagoranci zaman kwamitin bayar da shawara kan bayar da damar zama ɗan ƙasa, da aka gudanar a birnin Abuja.

A cewar ministan, an kafa kwamitin ne domin tantance wa da kuma bayar da shawarwari kan bukatar neman zama dan kasa ga wadanda suka nemi hakan, kafin amincewa da su.

Kwamitin dai ya hada da manyan jami’an gwamnati daga Ma’aikatar Shari’a, Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje, Hukumar Tsaro ta DSS, da Hukumar Shige da Fice ta NIS.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here