Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya cire sunan Maryam Sanda daga cikin jerin mutanen da aka tsara za a yiwa afuwar shugaban ƙasa.
Idan za’a iya tunawa kotu ce ta yanke wa Maryam Sanda, hukuncin kisa ta hanyar rataya a 2020 bayan ta same ta da laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello.
Mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin bayanai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba a Abuja.
A cewar sanarwar, shugaban ƙasa ya dauki matakin ne bayan ya tuntubi Majalisar Koli ta Ƙasa da kuma bayan ya duba ra’ayoyin jama’a game da jerin sunayen masu neman afuwa.
Tinubu ya ba da umarni cewa ba za a saka mutanen da aka tabbatar da manyan laifuka kamar kisa, garkuwa da mutane, safarar mutane, laifukan miyagun ƙwayoyi da zamba ba, a cikin jerin masu neman afuwa.
Sai dai sanarwar ta ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda ke cikin jerin da suka aikata irin waɗannan laifuka za a rage musu hukunci maimakon a soke afuwar gaba ɗaya.


