Rahoton Daily Trust ya nuna cewa rufe matatar mai ta Port Harcourt daga Mayu zuwa Oktoba 2025 ya jawo wa Najeriya asarar kimanin Naira biliyan 366.2.
An kashe dala biliyan 1.5 wajen gyaran matatar a 2021, kuma ta fara aiki a Nuwamba 2024, amma bayan watanni shida aka sake rufe ta saboda gyara da bincike.
Wasu ma’aikata sun ce matatar bata taba tace mai ba, inda ake kawo man da aka riga aka tace daga waje ana sayarwa a matsayin wanda aka tace a ciki.
Shugaban NNPCL, Bayo Ojulari, ya tabbatar da cewa kamfanin yana asarar miliyan 300 zuwa 500 a kowane wata saboda matsalolin kayan aiki.


