Majalisa ta amince shugaban ƙasa Tinubu ya ciyo bashin manyan kuɗaɗe
Majalisar Wakilai ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu ta neman rancen dala biliyan 2.35 domin cike gibi a kasafin kuɗin shekarar 2025.
Haka kuma majalisar ta ba da izinin fitar da takardar bashin Sukuk ta farko mai darajar dala miliyan 500 a kasuwar kuɗi ta ƙasa da ƙasa, domin aiwatar da manyan ayyukan gine-gine da kuma bunƙasa hanyoyin samun kuɗaɗen gwamnati.
Amincewar ta biyo bayan nazari da amincewar rahoton Kwamitin Majalisar kan Tallafi, Rance da Gudanar da Bashi a zaman majalisar na ranar Laraba.


