Kotu ta kulle matashin da ya kashe mahaifin sa a Kano
Babbar kotun jihar Kano mai lamba 7, karkashin jagorancin mai shari’a Amina Adamu, ta umarci a mayar da wani matashi mai suna Aminu Ismail, ɗan asalin garin Ganbai a karamar hukumar Ajingi, zuwa gidan gyaran hali bisa zargin kashe mahaifinsa, Dahiru Ahmad.
Rahotanni sun nuna cewa rikici ya barke tsakanin Aminu da mahaifinsa ne bayan tsohon ya hana shi ƙarin aure, lamarin da ake zargin ya kai ga kisan mahaifin nasa.
Lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba Sorondinki, ya nemi kotu ta karanta masa tuhumar da ake yi wa wanda ake zargi, amma Aminu ya musanta laifin gaba ɗaya.
Bayan sauraron ɓangarorin biyu, mai shari’a Amina Adamu ta ɗage cigaban shari’ar zuwa ranar 13 ga watan Nuwamba domin fara sauraron shaidu.
Rahotanni sun kuma tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a watan Afrilu 2024 bayan rikicin cikin gida da ya kunno kai tsakaninsu.


