Gwamnatin tarayya ta fitar da Naira biliyan 2.3 domin biyan bashin albashi da bashin ƙarin matsayi na malaman jami’o’i a wani ɓangare na kokarinta na kawo ƙarshen takaddama tsakaninta da ƙungiyoyin malaman jami’a.
Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya ce an biya kuɗin ne ta ofishin Akanta Janar na Ƙasa a matsayin rukuni na takwas na biyan bashin da malaman jami’o’i ke bin gwamnati. Ya ce jami’o’in da abin ya shafa za su fara samun saƙon biyan kuɗaɗen daga yanzu kowane lokaci.
Sai dai wasu daga cikin malaman sun bayyana cewa har yanzu ba su karɓi albashin watan Oktoba ba, duk da sanarwar gwamnati.
Ƙungiyar ASUU ta sha yin takaddama da gwamnati kan batun bashin albashi, ƙarin matsayi, da kuma ƙarancin kuɗin da ake ware wa jami’o’i. Kwanan nan ta dakatar da yajin aikin mako biyu bayan shiga tsakani daga NLC da Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
Malaman na buƙatar gwamnati ta biya musu albashin watanni uku da rabi da aka rike, tare da aiwatar da yarjejeniyar da aka sake nazari a 2009 da kuma samar da kuɗaɗen farfaɗo da jami’o’i.


