Shugaban Kwamitin Tsaron Cikin Gida na Majalisar Wakilai, Hon. Garba Muhammad, ya bayyana cewa an samu barazanar harin bam daga ‘yan bindiga zuwa ginin Majalisar Dokoki.
Da yake magana yayin zaman sauraron ra’ayoyin jama’a kan kudirin dokar kafa Hukumar Tsaron Majalisar Dokoki, Garba ya jaddada muhimmancin kafa hukumar domin ƙarfafa tsaro a majalisar wacce ke zama cibiyar dimokuraɗiyya.
A cewarsa, kafa hukumar zai taimaka wajen kula da tsare-tsaren tsaro, da kare sanatoci, ‘yan majalisa, ma’aikata da kuma baƙi da ke shiga harabar majalisar.
Ya bayyana cewa majalisar na fuskantar ƙalubale da dama na tsaro, kamar satar motoci da babura, lalata kayayyaki, amfani da takardun shaida na ƙarya, da kuma shiga majalisar ba tare da izini ba.
“Mun samu rahoton cewa wasu ‘yan bindiga na shirin kai harin bam a majalisar dokoki, haka kuma wasu masu zanga-zanga na shirin toshe majalisar,” in ji shi.
Ya kuma nuna damuwa cewa wasu ‘yan majalisa na fuskantar barazana daga al’ummarsu da kuma wasu mutane da ke shiga ofisoshinsu ba tare da bin tsarin tsaro na hukuma ba.


