’Yan bindiga sun sake kai hari a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina, inda suka kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da wasu mutum 15 a wasu kauyuka guda shida.
Lamarin ya faru ne duk da yarjejeniyar sulhu da aka yi da wasu daga cikin ’yan bindigar, abin da ya sa mazauna yankin ke rayuwa cikin tsoro da fargaba.
Wasu mazauna sun ce hare-haren sun zama ruwan dare, inda ’yan bindigar ke kashe mutane da sace dukiya ba tare da tsoron hukuma ba.
Rahotanni sun nuna cewa mutane da dama sun tsere zuwa Dutsen Rimi da hedikwatar karamar hukumar domin neman mafaka.
Shugaban karamar hukumar Bakori, Abubakar Musa Barde, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an tuntubi waɗanda aka yi sulhu da su, amma sun musanta hannu a harin.


